22 Disamba 2021 - 13:26
​Faransa Ta Sanar Da Hallaka Wani Jigon Kungiyar IS, A Nijar

Rundinar sojin faransa ta ce ta hallaka wani kwamanda na reshen kungiyar IS, a yankin babban sahara, a Nijar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Sanarwar da rundinar ta fitar ta ce Soumana Boura, na daya daga cikin wadanda suka kashe faransawa shida ‘yan agaji da masu musu rakiya biyu ‘yan Nijar a yankin Koure a cikin watan Agusta 2020.

An bayyana mutumin a matsayin mamba na kungiyar IS a yankin sahara, kuma an kashe a wani harin jirgi marar matuki a ranar Litini data gabata, lokacin da yana kan babur dinsa.

An kuma yi aikin tare da hadin guiwar hukumomin Nijar, inji sanarwar rundinar sojin ta faransa.

Dama dai kwanakin baya faransa ta sanar da hallaka shugaban kungiyar ta IS a yankin babban sahara Adnan Abou Walid Al Sahraoui, da ta dauki alhakin kashe faransawan, sannan kuma a Nijar an cafke mutane da dama da ake zargi da hannu a harin.

342/